Yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama ne aka sanya hannu kansu a ranar Talata a birnin Yamai tsakanin shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou da takwaransa na Iran Mahmoud Ahmadinejad a yayin ziyarasa a kasar Nijar.
Da yake bude zaman taron aiki, shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, bayan ya bayyana jin dadinsa da zuwan takwaransa na kasar Iran a kasarsa.
Mista Issoufou ya yi amfani da wannan dama domin tunatar da cewa, musanya tsakanin kasashen biyu tana zama tushen samun makoma mai kyau ga cigaban dangantaka a fannonin daban daban, musammun ma hanyoyi ne dake budewa bangaren masu zaman kansu a kasar Nijar.
Shugaba Issoufou ya bukaci ma'aikatun kasuwanci na kasashen biyu da su gaggauta kafa wani kwamitin hadin gwiwa kan harkoki tsakanin Nijar da Iran.
Haka kuma shugaban kasar Nijar ya bukaci shugaba Ahmadinejad da ya taimaka wajen cimma tsarin cigaban tattalin arziki da na jama'a na kasar Nijar (PDES 2012-2015), tsarin koyi guda da kasar Nijar ta kirkiro domin kulawa da gaba dayan ayyukan masu tallafawa kasarsa.
Yawaita da fadada dangantakar abokantaka, sada zumunci da hulda tsakanin kasashen musulmi tushe ne na cigaban al'ummomi, kana babban zarafi na bunkasa zaman lafiya, kwanciyar hankali da tsaro a duniya, in ji shugaban kasar Nijar. (Maman Ada)