in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Har yanzu ba'a samu daidaituwar al'amura ba a Kivu, DRC, in ji mai magana da yawun MDD
2012-12-06 10:37:51 cri

Mai magana da yawun magatakardan MDD Martin Nesirky ya yi bayani ranar Laraba cewa, har yanzu ba'a samu daidaici ba a yanayin da ake ciki a jamhuriyar demokrdaiyar Congo DRC, ganin cewar ana zaman kila wa kala a yankunan Kivu guda biyu, duk ko da cewar 'yan tawayen M23 suna janye dakarunsu sannu a hankali.

Yayin da yake jawabi da aka saba yi ga manema labarai, Mr Nesirky ya ce, ana ci gaba da janye dakarun M23 a yankin arewacin Kivu.

Ya kara da cewa, an fara tura dakarun gwamnatin kasar Congo zuwa Sake, dake yamma da Goma, babban birnin arewacin Kivu.

A kuma yankin kudancin Kivu, cibiyar MDD dake aikin daidaita al'amura a DRC (MONUSCO) na ba da tallafi ga sojojin gwamnatin jamhuriyar demokradiyar Congo, FARDC don mai da martini ga 'yan tawaye a yankunan Bunyakiri, Hombo da Kilembwe.

Mai magana da yawun MDD ya ci gaba da cewa, duk da janyewar dakarun M23 da kuma alamun da ake gani na daidaito, a har yanzu akwai babbar damuwa dangane da aikin ba da agaji da samar da kariya a arewacin Kivu.

Mr. Nesirky ya ba da misali da yadda wasu 'yan bindiga suka diram ma sansanin Mugunga na uku, wanda ke dauke da 'yan gudun hijira sama da dubu 30, tsakanin ran daya zuwa biyu ga watan Disamba cikin dare, suka yi kwace karfi da yaji a sansanin.

Baya ga hakan, an kuma samu rahoton fyade guda 70 a cibiyoyin lafiya dake Minova.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China