Kungiyar AU ta gudanar da wani taro na musamman a birnin Addis Ababa na kasar Habasha ranar Talata 8 ga wata, domin tattauna batutuwan da suka shafi aika rundunonin sojin samar da zaman lafiya zuwa jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, a wani mataki na aiwatar da tsare-tsaren dawo da tsaro a yankunan kasar dake fama da barazanar ayyukan 'yan tawaye. Wannan dai taro da kwamishinan kungiyar mai lura da harkokin tsaro da samar da zaman lafiya Ramtane Lamamara ya jagoranta, wanda kuma ya samu halartar ministocin waje, da na tsaro na kasashe mambobin kungiyar, da ma wakilan kungiyoyin bunkasa ci gaban sassan nahiyar ta Afirka da suka hada da kungiyar SADC, da CEEAS da kuma ICGLR, ya zamo ci gaba, kan taron tuntubar juna da ya gabata, wanda ya mai da hankali ga bin hanyoyin aiwatar da matakan mai do da tsaro a lardin arewacin Kivu, dake gabashin kasar. Da yake jawabi gaban mahalarta taron, jami'i mai baiwa babban sakataren MDD shawara kan harkokin soji, Janar Babacar Gaye, bayyana matsayar MDD ya yi, don gane da aiwatar da kudurin da kwamitin tsaro ya cimma na shekarar 2012. wannan kuduri, a cewar Gaye ya tanadi irin rawar da majalisar za ta taka a nan gaba, wajen tabbatar da nasarar ayyukan rundunar MONUSCO bisa bukatar da kasashen Afirkan suka gabatar, ta neman tallafin majalisar na samar da tallafin rundunonin sojin-sa-kai a jamhuriyar ta dimokaradiyyar Congo.(Saminu)