in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire na cigaba da fuskantar kalubaloli, in ji wani jami'in MDD
2013-04-17 11:02:25 cri

Kasar Cote d'Ivoire na cigaba da fuskantar kalubaloli, duk da cigaban da aka samu tun bayan kawo karshen rikicin zabe yau da shekaru biyu, in ji wani jami'in dake kula da ayyukan tabbatar da zaman lafiya na MDD, mista Edmond Mulet.

A cikin wadannan kalubaloli, akwai matsalar dakaru masu makamai, laifuffukan kasa da kasa, ta'addanci, fashi da rashin cikakken gyaran fuska ga bangaren tsaro, in ji mista Mulet wanda ya gabatar wa kwamitin sulhu na MDD wani sakamakon bincike kan rikicin kasar Cote d'Ivoire.

Wannan bincike ya bukaci da karfafa hanyoyin hadin gwiwa tsakanin tawagar MDD dake Cote d'Ivoire (ONUCI) da tawagar MDD dake Laberia (MINUL) da kuma halin aiwatar da dabarar da ta shafi kare fararen hula.

Mista Mulet ya tabbatar da cewa, matsalar tsaro a yankin iyaka ta samu dan kyautatuwa sakamakon dangantaka mai kyau tsakanin Abidjan da Monrovia, har game da tura sojojinsu da jami'an tsaronsu a kan tsawon iyaka.

Binciken ya yaba da kokarin gwamnatin kasar Cote d'Ivoire na bude kofa ga 'yan adawa da kuma fara shawarwarin kai tsaye tare da tsofuwar jam'iyyar dake mulki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China