Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamoud ya yi Allah wadai a ranar Lahadi da harin da aka kai kan kadarorin gwamnatin Somaliya a birnin Mogadishu a ran nan. Wasu mutane rike da makamai sun kai hari kan wasu ma'aikatun gwamnati dake birnin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 20, ciki har da 9 daga cikin wadanda suka kai harin. Haka kuma an gano cewa, akwai 'yan kunar bakin wake daga cikin mutanen da suka kai harin na Mogadishu.
'Harin ya nuna cewa, 'yan ta'addan da suka rasa dukkan sansanoninsu za su zo karshensu a kasar Somaliya', in ji shugaba Hassan.
Haka kuma ya bayyana cewa, wasu 'yan tsirarrun mutane ba za su hana kasar Somaliya ta samu cigaba ba, ba wanda zai hana wannan yunkuri na cimma sahihin buri, na kasar Somaliya mai zaman lafiya da jituwa.
Faraministan Somaliya Abdi Farah Shirdon ya ce, hallaka mutanen Somaliya ba shi da wata alaka da addinin Islama.
Haka kuma ya kara da cewa, wannan bala'i ne ga dukkan mutanen da lamarin ya shafa. Haka na nuna cewa, abokan gabarmu na kusan karshensu kuma suna ja da baya daga kasar Somaliya.
'Yan tawayen Shebab sun yi shelar daukar alhakin kai wannan hari na Mogadishu, wanda ya faru kwanaki kadan bayan gwamnatin Burtaniya ta yi kashedi kan hare-haren ta'addanci a Mogadishu, babban birnin kasar. (Maman Ada)