in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Morsi ya yi watsi da tattaunawa da wadanda suka sace mutane
2013-05-20 10:29:09 cri

A ranar Lahadi, shugaban kasar Masar Mohammed Morsi ya yi watsi da batun tattaunawa da wadanda suka sace sojoji guda bakwai a Sinai, wadanda aka nuna su ta bidiyo ta intanet domin neman a sako su.

Kamfanin dillancin labaran kasar Masar MENA ya ba da rahoton cewa, shugaba Morsi yayin wata ganawa da shugabannin jam'iyyun siyasa da dama don tattaunawa kan batun kokarin sako sojojin bakwai da wasu 'yan bindiga suka sace a arewacin Sinai, yana mai cewa, ba zai tattauna da masu aikata laifi ba.

A cikin hoton, daya daga cikin wadanda aka sace wanda wani da ba'a ganin fuskarsa ke zungurarsa da bindiga ya ce, wadanda suka sace suna bukatar a sako wadanda ke daure saboda dalilai na siyasa a Sinai, ciki har da Hamada Abou Sheita wanda a kai wa daurin rai da rai bayan an same shi da laifin kai hari a tashar 'yan sanda a shekarar 2011 a Sinai.

Kafar watsa labaran kasar ta shafin intanet, Ahram ta ba da rahoton cewa, ma'aikatar harkokin cikin gida na dubawa da kuma tantance hoton bidiyon.

A ranar Alhamis, wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiya masu tsatsauran ra'ayin Jihadi ne, sun sace wasu jami'an tsaro bakwai, hudu sojoji, uku 'yan sanda, a yankin Green Valley na Sinai mai nisan kilomita ashirin daga birnin Arish, inda kujerar gwamnati ke da zama.

A kuma ranar Asabar, wata kafar leken asiri ta soji ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewa, hukumomin kasar Masar sun dakatar da tattaunawa da wadanda suka sace mutanen saboda dimbin bukatu da suka gabatar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China