Shugaban kasar Masar Mohammed Morsy a jiya Talata 7 ga wata ya rantsar da sabbin ministoci 9 a wani gyaran fuska da ya yi ma gwamnatinsa wanda a ciki, akwai manyan mukamai da suka shafi tattalin arziki.
A jawabinsa, Morsy ya bayyana cewa, wannan gyaran fuskar da aka yi wani sabon mataki ne da zai kammala shirin inganta ayyukan al'ummar kasar, kuma an yi shi ne da zummar kawo sabbin jini a cikin gwamnati domin su taimaka a samar da abubuwan da jama'ar suke fatan samu na cigaba.
A cikin wata sanarwa daga fadar shugaban, ya bukaci al'ummar kasar da su ba da dama ga sabuwar gwamnatin da aka yi ma gyaran fuska domin aiwatar da ayyukan da aka dora mata, da kuma fuskanci kalubalolin dake gabanta.
Sai dai wannan gyaran fuska ya ba da damar shigar da karin 'ya'yan jam'iyyar 'yan uwa musulmi wato MB, wadanda suka hada da ministan kudi Fayyad Abdel-Monem Hassanin, wani shaihun malami a jami'ar Al-Azhar, da kuma ministan huldodin kasashen waje da tsare-tsare Amr Darrag wanda shi ma babban 'dan jam'iyyar neman 'yanci da adalci ne wato FJP wanda wani reshe ne na jam'iyyar 'yan uwa musulmi MB.
Ana dai ganin wadannan ministocin biyu suna da matukar muhimmanci wajen tattaunawar da kasar take shirin yi da asusun ba da lamuni ta duniya IMF domin neman rancen kudi dala biliyan 4.8 da ake ganin zai taimaka a farfadowar tattalin arzikin kasar.
Ministan cikin gida dai ya tsallake a wannan gyaran fuska, duk da irin sukar da ya rika fuskanta daga 'yan adawa.
Babban kungiyar adawar kasar NSF 'National Salvation Front' tana son shugaba Morsy ya kafa gwamnatin da zai tafi da kowa ba tare da banbancin komai ba, don haka, ta bukaci babban mai shigar da kara na kasar wanda 'dan jam'iyyar 'yan uwa musulmi ne kafin zaben 'yan majalissar dokoki da za'a yi a watan Oktaban bana.(Fatimah)