in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai baiwa shugaba Morsi shawara kan harkokin shari'a ya mika takardar yin murabus
2013-04-24 10:38:26 cri

A ranar Talata ne mai baiwa shugaban kasar Masar shawara kan harkokin shari'a Fouad Gadallah ya mika takardarsa ta yin murabus bisa dalilan cewa, babu wani haske game da tafiyar da kasar da kuma yadda aka tsara makomar kasar ta Masar.

Jaridar Al-Ahram ta ruwaito Fouad Gadallah yana cewa, baya ga wadancan dalilai, an kuma dage kan ganin daurewar gwamnatin firaminista Hesham Qandil, duk da cewa ta gaza a bangaren harkokin siyasa, tattalin arziki da kuma harkokin tsaro, sannan an yi yunkurin kashe bangaren shari'a, da kushewa sashen 'yanci, tare da yin watsi da hukuncin da ya yanke.

Gadallah ya ce, kamata ya yi a baiwa bangaren shari'a 'yanci kuma bai kamata a rika tsomawa sashen baki ba.

Bugu da kari, a ranar Lahadi ma ministan shari'a na kasar Masar Ahmed Mekki shi ma ya mika takardarsa ta yin murabus, saboda zanga-zangar baya-bayan da masu kishin Islama suka yi, inda suke kiran da a soke bangaren shari'ar kasar.

Sai dai yayin da yake bayyana yin murabus din nasa, Mr. Gadallah ya bayyana hadarin da kasarsa ke ciki, inda ya yi kira ga jam'iyyun adawa da masu kishin Islama da takwarorinsu masu sassauci da tsattsauran ra'ayi da su zauna kan teburin sulhu, kana su hada kai don amfanin Masar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China