Kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA ya bayar da rahoto a ranar Lahadi cewa, kotun kasar Masar ta kebe ranar 2 ga watan Yuni domin ta yanke hukunci na karshe game da matsayin majalisar shura a hukumance da kuma majalisar dokokin kasar wadda ta tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar.
Kotun ta yanke wannan shawara ce bayan da kotun kolin kasar ta yi nazarin karar da aka shigar game da matsayin dokar da ta bayar da iznin zabar majalisar shura a hukumance, da kuma majalisar dokokin kasar.
An rabi kashi biyu bisa uku na mambobin majalisar shura 270 masu ra'ayin Islama ne, yayin da saura 90 kuma shugaba Morsi ne ya nada su a karshen watan Disamba.
A watan Yuni na shekara ta 2012, kwanaki kadan kafin a zabi Morsi a matsayin shugaban kasa, kotun kolin kasar ta yanke hukunci rushe majalisar shura, majalisar dokoki, wadda bisa al'ada take rike da ikon majalisa, matakin da kotun ta ce, ya sabawa doka.(Ibrahim)