Ministan shari'ar kasar Masar Ahmed Mekki, ya mika takardar yin murabus daga aikinsa ga shugaba Mohamed Morsi, da firaminista Hesham Qandil a ranar Lahadi 21 ga watan nan.
Kamfanin dillanci labarun kasar Masar MENA ne ya rawaito hakan, yana mai cewa, lamarin na zuwa ne kwana guda, da gudanar zanga-zangar da daruruwan magoya bayan kungiyar 'yan uwa Musulmi dake kasar suka gudanar a harabar ginin babbar kotun kasar, inda suka bayyana rashin jin dadinsu, ga tafiyar wahainiya da shari'ar tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak ke yi, tare da wanke wasu daga jami'an da suka yi aiki karkashin tsohuwar gwamnatin da kotu ta yi, lamarin da suka bayyana da aiki, irin na gurbataccen tsarin shari'a.
Cikin takardar da ya mika ga ofishin fadar gwamnati, Mekki ya yi fatan cewa, shugaba Morsi zai yarda da bukatarsa ta sauke wannan babban nauyi dake wuyansa.
Don gane da wannan lamari, mai magana da yawun gwamnatin kasar Alaa Al-Hadidi, ya ce, Mekki zai kasance kan mukaminsa, har izuwa lokacin da shugaban kasar zai nada sabon jagoran ma'aikatar, karkashin shirin da ake yi na yiwa majalissar zartaswar kasar garan-bawul.
A ranar Asabar din da ta gabata ne dai shugaba Morsi ya bayyana aniyarsa ta yiwa majalissar zartaswar kasar gyaran fuska, matakin da ya ce ba shi da wata alaka da bukatar wani bangare na 'yan adawa.(Saminu)