in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria ta goyi bayan kudurin MDD na aika sojojin Afirka zuwa Mali
2012-12-24 10:28:07 cri

Kasar Algeria ta bayar da sanarwa a ranar Lahadi cewa, ta goyi bayan kudurin MDD da ke bayar da umarnin aikawa da dakarun shiga tsakani na kasa da kasa karkashin jagorancin Afirka zuwa kasar Mali,

Ministan harkokin wajen kasar Algeria Amar Belani ya bayyana cewa, "Wannan kuduri ya jaddada muhimman matakan da suka wajaba a dauka na warware rikici kasar ta Mali, ciki har da babbar rawar da 'yan kasar ta Mali za su taka cikin shirin da nufin kawar da matsalar kwata-kwata tare da bayyanawa karara cewa, kungiyoyin Aqim da Mujao manyan barazana ne ga shiyyar baki daya."

Belani ya ce, Algeria ta nanata kudurinta na ci gaba da kokarin da take yi wajen ganin an cimma sassantawa tsakanin 'yan kasar Mali, samar da taimakon jin kai da bayar da gudummawar maido da ikon yankunan kasar. Jami'in ya ce, kamata ya yi duk wani matakin soja da za a dauka a kasar ta Mali, ya mayar da hankali kan kungiyoyin 'yan ta'adda da masu aikata miyagun laifuffuka, domin a cewarsa, an bayyana wadannan ka'idoji karara a cikin kudurin MDD, kuma ta haka ne kwalliya za ta biya kudin sabulu, ciki har da batun tsare-tsare, hanyoyin tattara kudade, da bayar da tabbaci ga kare rayukan farare hula yayin da ake daukar matakan.

Ko da yake Algeria ta damu matuka cewa, aikin shiga tsakanin na Mali na iya kara yawan 'yan gudun hijiran Mali da za su kwarara zuwa iyakar kudancin kasarta.

Ministan cikin gida na kasar Algereia Daho Ould Kablia, ya ce, a makon da ya gabata, Algeria ta tsugunar da 'yan gudan hijirar Mali 25,000 wadanda suka gujewa tashin hankalin da ake a kasarsu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China