Ministan harkokin cikin gida na kasar Algeria Daho Ould Kablia ya bayyana ran Alhamis cewa, kasar ta karbi bakuncin 'yan gudun hijira 25,000 da suka bar kasashensu saboda rikice-rikice, wadanda akasarinsu 'yan kasashen Mali da Nijar ne.
Kamfanin dillancin labaran kasar, APS ta ce, Ould Kabila ya ce, saboda dalilai na jin kan bil adama, zai zamo da wuya, a yanzu haka a koma da 'yan gudun hijran zuwa kasashen nasu dake fama da rikice-rikice.
Ministan ya yi nunin cewa, gwamnatin kasar na kula da 'yan gudun hijran ne a cikin tantuna da aka kakkafa a yankunan kan iyakokin kasar, ana kuma masu tanadi da suka dace da yanayin rayuwa.
To, amma kuma kasar ta Algeria ta tusa keyar mutane da yawansu ya kai 41,078 da suka shigo kasar ba tare da izini ba, tsakanin shekarar 2009 da 2011, a matsayin wani yunkurin yaki da masu shigowa kasar dake arewacin Afirka, ba tare da izini ba.
Kasar ta damu matuka kan cewar, daukar matakin amfani da karfin soja a kasar Mali zai kara kwararowar 'yan gudun hijira a kan iyakar kudancin kasar daga Mali.(Lami)