in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda za su fito jefa kuri'a a Algeria zai kai kashi 40 zuwa 45 cikin dari
2012-11-21 09:59:23 cri

Ministan harkoki cikin gida da kananan hukumomi na kasar Algeria Daho Ould Kablia ya yi bayani ran Talatar nan cewa, ana sa rai cewar, yawan wadanda za su fito jefa kuri'a a zaben da za'a yi a ran 29 ga watan Nuwamba zai kai tsakanin kashi 40 zuwa 45 daga cikin dari.

Jam'iyyun siyasa guda 52 da 'yan takara masu daukar nauyin kansu ne ke fafatawa don samun kujeru guda 1541 na majalisun birane da kuma guda 48 na majalisun yankuna.

Ministan ya ce, wannan zabe zai yi kama da na babbar majalisar kasar, inda aka samu fitowar masu jefa kuri'a tsakanin kashi 40 zuwa 45 daga cikin dari.

Jami'in gwamnatin ya ci gaba da cewa, gwamnatin kasar ta Algeria ta yi kyakkyawan tanadin tabbatar da nasarar zaben.

A lokacin zaben yankunan kasar da aka yi a shekarar 2007, jam'iyyar National Liberation Front (FLN) da jami'yyar National Democratic Rally (RND) ne suka yi nasarar samun kujeru mafi yawa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China