in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala kananan zabukan kasar Algeria lami lafiya
2012-11-30 10:30:24 cri

Al'ummar kasar Algeria sun kammala kananan zabukan kasar da suka hada da na wakilan kananan hukumomi masu mambobi 1541 da na wakilan larduna 48 lami lafiya. Zabukan da aka kammala ranar Alhamis din nan, wadanda yawan masu jefa kuri'ar da aka yiwa rijista suka kai 21,445,621 dai na cikin muhimman matakan tabbatar tsarin mulkin dimokaradiyyar kasar. A cewar ministan cikin gidan kasar Daho Ould Kablia, al'umma sun gudanar da zabukan cikin kyakkyawan yanayi, inda alkaluman zaben suka nuna kimanin kaso 44.26 na masu jefa kuri'u ne suka kada kuri'unsu yayin zaben wakilan kananan hukumomi, yayin da zaben wakilan larduna ya samu kaso 42.92 na adadin masu kada kuri'u, adadin da a cewar ministan ya kai na makamancinsa da ya gabata a shekarar 2007.

Manyan jami'an gwamnatin kasar, ciki hadda shugaba Abdelaziz Bouteflika, da firaminsta Abdelmalek Sellal, sun kasance cikin dubban al'ummar da suka samu kada kuri'unsu. A tabakin firaminista Sellal, ayyukan 'yan majalisun za su taimaka matuka, wajen ciyar da rayuwar al'ummar kasar gaba.

Ana dai sa ran a Juma'ar nan ne Kablia, zai kira taron manema labaru, inda zai bayyana sakamakon zaben a hukumce.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China