Kamfanin dillancin labaran kasar Algeria APS ya ba da rahoto jiya ran 11 Alhamis cewar, ma'aikatar kudi da bankin kasar Algeria sun ba da wata sanarwa da ke nuni cewa, kasar ta Algeria za ta ba da gudummawar dalar Amurka biliyan biyar na rance ta hanyar sayen hannayen jari na musamman SDR ga asusun ba da lamuni na duniya IMF.
A fadin sanarwar, "Wannan wata kyakyawar dama ce ga Algeria don za ta samu fadada jarinta, ta kuma rage barazanar yawan faduwa ko haurawar kudin ruwa, sannan za'a samu daidaito kan hannayen jarin na musamman ganin cewa, za ta haifar da riba da ya yi daidai ko kuma ya wuce na tsarin babban lamuni."
Tun farkon shekarar nan ne asusun ba da lamunin IMF, ke neman kara yawan kudin da aka ware don bayar da su rance, da dalar Amurka biliyan 500.
A cikin watan Afrilu, ministan kudi na Algeria Karim Djoudi ya ce, IMF ta nemi taimako, daga kasar Algeria don kara inganta matsayinta na kudade.
Djoudi wanda ke bayani bayan wata ganawar asusun ba da lamunin da babban bankin duniya a birnin Washington cikin watan Afrilu, ya ce, asusun ba da lamunin ya gabatar da wannan bukata ne ga Algeria a matsayinsa na kasa dake da rarar kudade, da nufin bunkasa albarkatun asusun don ya samu ba da rance ga kasashe mabukata.(Lami)