Kamfanin dillancin labaran Algeria APS ya ba da rahoton cewa, yayin wata ziyara, sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka Hillary Clinton ta gana da shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika dangane da batutuwan yankin, musamman ma game da yanayin da ake ciki a kasar Mali.
Clinton ta bayyana wa manema labarai bayan ganawar da ta yi da shugaba Bouteflika cewa, "Mun yi tattaunawa filla-filla dangane da yanayin da ake ciki a yankin Sahel, musamman ma a arewacin kasar Mali."
Ganawar tasu ta mai da hankali ne kan batun ta'addanci da fataucin miyagun kwayoyi a yankin, in ji Clinton wace ta fara ziyarar aiki a kasar Algeria daga safiyar ranar Litinin.
Wannan ziyarar da Clinton ta kawo ta biyo bayan wata muhimmiyar tataunawa ne da aka yi tsakanin Algeria da Amurka a ran 19 ga watan Oktoba a birnin Washington.
Clinton ta kawo ziyara a baya, a birnin Algiers ran 25 ga watan Fabrairu a matsayin wani bangaren ziyara da ta kawo yankin na Maghreb.(Lami)