in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa hukumar kula da aikin sadarwa ta CSC a kasar Nijar
2013-04-04 10:50:00 cri

Babbar hukumar sadarwa ta CSC, hukuma ce mafi girma dake kula da aikin jarida a kasar Nijar, aka yi bikin kafa ta a ranar Laraba a zauren babban kotun kasa dake birnin Niamey, kuma za ta gudanar da aiki bisa wa'adin shekaru biyar kawai. Hukumar CSC, hukuma ce mai zaman kanta da dokar kasa ta amince da aikinta na sanya ido kan aikin jarida a kasar Nijar a ranar 25 ga watan Nuwamban 2010, musammun ma a bangaren kafofin mujallu da jaridu, internet, rediyo da talabijin, da kuma tallace-tallace ta hanyar kafofin watsa labarai.

Hakazalika aikin CSC shi ne samar da tabbatar da 'yancin fadin albarkacin baki da 'yancin samun kayayyakin sadarwa na rediyo da talabijin, ga kafofin jaridu da na internet, domin haka, wajibi ne hukumar CSC ta sa ido kan aikin jama'a da aka mikawa kafofin gwamnati, da girmama sharudan watsa labarai da sadarwa, tare kuma da bai wa kowa ne 'dan kasa, kungiyoyi da jam'iyyun siyasa damar amfani da wadannan kafofin gwamnati, da kuma 'yancin fadin albarkacin baki a cikin kafofi masu zaman kansu bisa adalci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China