in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zuma ya yi kira da a kafa wani yankin musanya cikin 'yanci na bangarori uku a Afrika
2013-05-08 11:09:38 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya yi kira a ranar Talata da a rubunya kokarin kafa wani yankin musanya cikin 'yanci na bangarori uku a nahiyar Afrika domin bunkasa dangantakar tattalin arziki da harkokin musanya masu karfi tsakanin kasashen Afrika.

Matakin kafa wannan yankin musanya cikin 'yanci na bangarori uku na nahiyar zai ba da kwarin gwiwa ga kamfanoni masu zaman kansu da su kara zuba jari a nahiyar Afrika, in ji Jacob Zuma a yayin wani dandalin harkokin kasuwanci tsakanin Afrika ta Kudu da Najeriya a birnin Cape Town.

Dandalin ya gudana kafin ziyarar shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan a kasar Afrika ta Kudu.

Yankin musanya cikin 'yanci zai hada kasuwa guda ta kuriyar Afrika da tsakiyar Afrika, gamayyar cigaban kuriyar kasashen Afrika da gamayyar kasashen gabashin Afrika. Kuma yanki ne mafi girma na Afrika ta kasuwa guda a wannan nahiya da aka kiyasta ga dalar Amurka biliyan guda.

Kasashen Afrika 26 da abun ya shafa suna da GDP na kusan dalar Amurka biliyan 860 da yawan al'ummomin da ya kai miliyan 600. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China