Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, ya zabi tsohon ministan cinikayyar kasar Kenya Mukhisa Kituyi domin ya shugabanci taron harkokin cinikayya da ci gaba na MDD(UNCTAD).
Wata sanarwa da taron na MDD ya bayar ranar Alhamis ta ce, idan babban zauren MDD ya amince da zabin, Kituyi zai shugabanci taron na wa'adin shekaru hudu wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumba.
Mr. Ban ya fada cikin sanarwar cewa, ya zabi Mukhisa Kituyi, 'dan kasar Kenya a matsayin babban sakataren taron na UNCTAD na tsawon wa'adin shekaru hudu daga ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa.
Ana sa ran Kituyi wanda shi ne shugaban cibiyar kula da harkokin shugabanci ta kasar Kenya ya maye gurbin Supachai Panitchpakdi, 'dan kasar Thailand wanda ya samu wannan mukami a ranar 1 ga watan Satumbar shekara ta 2005, kana aka sake zabarsa a shekara ta 2009.
Sanarwar ta ce, Supachai ya rike wannan mukami na tsawon shekaru 8, kuma zai kammala wa'adinsa na biyu na tsawon shekaru 4 a ranar 31 ga watan Agusta.
Shi dai tsohon masanin harkokin shari'a, 'dan kasar ta Kenya, ya yi karatun digirinsa na farko ne a fannin ilimin kimiyyar siyasa da dangantakar kasa da kasa a jami'an Makerere da ke Uganda, ya kuma yi karatun digiri na biyu a fannin zamantakewar al'umma, sannan ya yi karatun digirinsa na uku a fannnin falsafa, difloma a kimiyya, tsare-tsaren samar da kayayyaki, dukkansu a jami'ar Bergen da ke kasar Norway. (Ibrahim)