A ranar Litinin ne kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan munanan hare-haren bama-baman da aka dasa a mota da aka kai a wani gari da ke kan iyaka da kasar Turkiya a ranar Asabar, harin da ya halaka a kalla mutane 46, kana wasu da dama suka jikkata.
A cikin wata sanarwa da kwamitin mai mambobi 15 ya bayar, sun bayyana juyayinsu tare da mika sakonsu na ta'aziya ga iyalan wadanda harin ya shafa da kuma gwamnati da al'ummar Turkiya.
Sanarwar ta ce, duk wani nau'in ta'addanci yana haddasa mummunar barazana ga harkokin zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, sannan duk wani nau'in ta'addanci mumunan laifi ne kuma ba za a amince da shi ba, ko da mene ne manufarsu, inda aka aikata da kuma wanda ya aikata hakan.
Sanarwar ta ce, mambobin kwamitin sun nanata kudurinsu na kawo karshen duk wani nau'in ta'addanci bisa ka'idojin MDD. Bugu da kari kwamitin sulhun MDD ya tunatar da mambobin kasashen kwamitin cewa, wajibi ne matakan da suke dauka na kawar da ayyukan ta'addanci su dace da dokokin kasa da kasa musamman dokokin kare hakkin bil-adama, 'yan gudun hijira da harkokin jin kai na kasa da kasa. (Ibrahim)