Babban magatakardar MDD Mr. Ban Ki-Moon, ya bayyana farin cikinsa, da nadin sabon babban daraktan kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO.
Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Mr. Moon ya ce, nadin Roberto Carvalho de Azevedo, kwararre a fannin harkokin diplomasiyya a wannan mukami, abu ne da ya dace matuka. Sanarwar ta kuma kara da cewa, kasancewar Azevedo tsohon wakilin din din din a kungiyar, zai ba shi damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata, tare da daukaka matsayin kungiyar zuwa mataki na gaba
Daga nan sai Moon ya bayyana fatan yin aiki kafada da kafada da sabon jagoran, musamman a fagen ganin an inganta, tare da habaka tsarin cinikayyar kasa da kasa, tare da samar da wadata, da daidaito, da kuma bunkasa ayyukan kakkabe fatara, da samar da cigaba a dukkanin fadin duniya baki daya.
Kungiyar ta WTO dai ta bayyana nadin Azevedo ne a matsayin sabon babban daraktan nata ranar Talata 14 ga wata, domin ya maye gurbin Pascal Lamy, wanda wa'adin aikinsa zai cika ranar 31 ga watan Agusta dake tafe.(Saminu)