in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon MDD ta yi kira da a tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya a CAR
2013-05-16 09:51:53 cri

Wakiliyar magatakardar MDD ta musamman a kasar Afirka ta Tsakiya CAR Margaret Vogt, ta yi kira ga kwamitin tsaron MDD, da ya samar da wata runduna ta musamman, wadda za ta gudanar da aikin dawo da doka da oda a kasar Afirka ta Tsakiya.

Vogt ta kara da kira ga kwamitin, da ya duba batun sanya takunkumi ga kungiyoyin 'yan tawayen kasar, saboda keta hakkokin bil'adama da suke yi. Wakiliyar magatakardar MDD ta gabatar da wadannan shawarwari ne ranar Laraba 15 ga watan nan, lokacin da take gabatar da wani rahoto gaban wakilan kwamitin na tsaro su 15. Nogt ta ce, halin da ake ciki a Afirka ta Tsakiya ba shi da kyau ko kadan, don haka ne ma ta bukaci aikawa dakarun Seleka kashedi mai karfi, kan irin ta'asar da ake aiwatarwa a kasar, ciki hadda wawashe dukiyoyiyn al'umma, da kisan fararen hula, da kuma sauyin gwamnati ba bisa ka'ida ba.

A baya ma dai, sai da babban magatakardar MDD, da babbar kwamishina mai lura da kare hakkin bil'adama Navi Pillay, suka bayyana damuwarsu game da tabarbarewar al'amura a wannan kasa. Yayin da ita ma jami'ar kotun hukunta laifukan yaki ta kasa da kasa ko ICC a takaice, Fatou Bensouda, ta yi kashedin cewa, ICC na bincike kan laifukan cin zarafin fararen hula da aka aikata a kasar ta Afirka ta Tsakiya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China