in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Warware rikicin Mali ya wuce batun kawar da barazanar tsaro a kasar, in ji Ban Ki-moon
2013-05-16 11:05:02 cri

Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ya tunatar da kalubalen siyasa da na tattalin arziki da kasar Mali za ta fuskanta a yayin wani taron kasa da kasa da ya shafi taimakawa cigaban kasar Mali mai taken "Gaba daya domin wata sabuwar kasar Mali" da ya gudana a ranar Laraba a birnin Brussels.

Kawar da barazanar tsaro a wannan kasa wani sashi ne na warware babbar matsalar da ta shafi rikicin kasar Mali, a cewar wata sanarwa da karamar mataimakiyar sakatare janar kuma jami'a a tsarin MDD kan samun cigaba, madam Rebeca Grynspan.

Ya kamata shugabannin kasar Mali su dauki niyyar kafa wani tsarin sasanta 'yan kasa na musammun domin maido da ikonsu da 'yanci a duk fadin kasar, da ba da hidima ga mutanen kasar da kuma hana wannan kasa sake kasancewa wani sansanin kungiyoyin 'yan kishin Islama, in ji mista Ban a cikin wannan sanarwa. Haka kuma ya bayyana aikin dake jiran tawagar kasa da kasa ta MDD kan kasar Mali (MINUSMA), kamar yadda kuduri mai lamba 2100 na shekarar 2013 na kwamitin sulhu ya tanada na nuna niyyar gamayyar kasa da kasa na taimakawa Mali wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro cikin dogon lokaci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China