A ranar Talata, magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya nanata aniyar majalisar na ba da cikakken goyon bayanta ga shirin mika mulki a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, CAR, yayin wata ganawa da praministan kasar, in ji wani mai magana da yawun MDD yayin jawabi ga 'yan jarida.
A yayin jawabin da MDD ta saba bayarwa ga 'yan jarida kowace rana, mai magana da yawun na MDD Martin Nesirky ya ci gaba da cewa, magatakardar ya gana da praministan CAR Nicolas Tiangaye ranar Litinin.
Ya ce, a yayin ganawar, magatakardar MDD ya nuna goyon baya matuka ga praministan da kuma iko da ya samu daga yarjejeniyar Lebreville da kuma ta N'Djamena.
Nesirky ya kara da cewa, magatakardar ya nanata kudurin MDD na ci gaba da ba da hadin kai ga shirin mika mulkin.
Yayin ganawar a fadin mai magana da yawun MDD, Mr. Ban ya nanata cewa, yana da muhimmanci a kafa hukumomi masu inganci, kana a shigar da jama'a don a samu cimma nasarar shirin mika mulki a kasar.
Magatakardar MDD har wa yau ya nanata damuwarsa dangane da ci gaba da take hakkin bil Adama a fadin kasar da kuma tabarbarewar yanayin zaman jama'a, inda ya kara da cewa, ya dace a daina wannan cin zarafi a kuma hukunta masu aikatawa.(Lami)