A ranar Alhamis ne dakarun tsaron Najeriya suka bayar da sanarwar sanya dokar hana fita a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar, sakamakon ayyana dokar ta bacin da shugaba Goodluck Jonathan ya yi a jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa.
Kakakin Birget ta 23 da ke Yola, Laftana Ja'afaru Nuhu ya fada cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafe cewa, an sanya dokar a jihar Adamawa ce daga karfe 6 na dare zuwa karfe 6 na safe agogon wurin. Don haka ya ce, ana kira ga dukkan jama'a da su mutunta dokar.
Jihar ta Adamawa dai tana daga cikin jihohi ukun da shugaba Jonathan na Najeriya ya kafa dokar ta bacin, inda ya umarci babban hafsan tsaron kasar Admiral Ola Ibrahim, da ya tura karin dakaru zuwa jihohin na Borno, Adamawa da kuma Yobe.
Wakilin Xinhua da ke jihar ya ce, harkokin kasuwanci da na yau da kullum na tafiya kamar yadda aka saba a garin na Yola, kuma ana iya ganin sojoji da 'yan sanda a muhimman wurare, suna sa-ido kan zirga-zirgar jama'a.
A halin da ake ciki, mazauna jihar ta Adamawa, sun bayyana kaduwa da makaki game da ayyana dokar ta bacin da shugaban kasar ya yi a jihar tasu, inda suka yi kira ga jama'a da su kasance cikin nutsuwa, kana su baiwa jami'an hadin kai, ta yadda gwamnati za ta cimma nasarar manufarta na dawo da zaman lafiya da tsaro.(Ibrahim)