Sojin ruwan Najeriya ta gano ta kuma lalata matatun man fetur guda 8 da aka kafa babu izini, kana ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin barayin mai ne, a ranar Litinin.
Wata sanarwa daga mai magana da yawun sojin Abdulsalam Sani, na mai bayyana cewa, sojojin ruwan sun gano da kuma lalata wani babban jirgin sufurin daukar man fetur da kuma kwale-kwale a karamar hukumar Ogu/Bolo, yayin da suke sintiri da suka saba a jihar Rivers dake kudancin kasar Najeriya.
A halin yanzu dai ana yi wa mutane biyu da aka cafke tambayoyi don a gano wadanda suka dau nauyinsu.
A matsayin sabon yunkurin kawar da satar man fetur da lalata bututun mai a yankin, sojojin ruwa za su ci gaba da kasancewa a dukkan hanyoyin ruwa ba dare ba rana.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, sojin ruwan na shawartar barayin man su nemi hanyar neman halaliyarsu maimakon yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa ta hanyar satar man fetur.
Mai magana da yawun sojin ruwa ya kuma bukaci jama'a da su kawo rahoton, duk wanda yake da hannu a satar man fetur da lalata bututun mai ga jami'an tsaro.(Lami)