in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun fara yunkurin kawar da ayyukan 'yan ta'adda a kasar
2013-05-16 09:58:42 cri

A ranar Talata ne dakarun tsaro a Najeriya suka fara gudanar da ayyukan sintiri a kokarin kawar da ayyukan ta'addanci, kwana guda bayan da kasar da ke yammacin Afirka ta dauki wasu tsauraran matakai a jihohi uku da ke arewacin kasar.

A ranar Talata ne shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci a jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa don maido da harkokin tsaro a wuraren.

A cikin wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaron kasar Birgediya Janar Chris Olukolade wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafe, ya bayyana cewa, sojoji, 'yan sanda da sauran jami'an tsaro sun fara gudanar da ayyukansu a wadannan jihohi kamar yadda shugaban kasar ya bayar da umarni.

Idan ba a manta ba, a ranar Talata ne shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya baiwa babban hafsan tsaron kasar Admiral Ola Ibrahim umarnin da ya tura karin dakaru zuwa jihohin Borno, Adamawa da kuma Yobe.

Olukolade ya ce, dakarun za su mayar da hankali ne kan murkushe bata gari a yankunan da ke kan iyakokin wadannan jihohin da ake samun tashin hankali, kuma za a rika tura dakaru da kayan aiki.

Ya ce, manufar shirin ita ce tabbatar da ikon cikakkun yankunan kasar tare da inganta matakan tsaro a gine-ginen gwamnati a dukkan yankunan da ke kan iyakokin kasar.

Sanarwar ta ruwaito kakakin na cewa, an umarci dakarun da ke gudanar da wannan aiki game da damke, gudanar da cikakken bincike, musamman su damke wadanda suka karya dokokin ikon cikakkun yankunan kasar ta hanyar tayar da keyar baya da sauran ayyuka dangin wadannan.

Bugu da kari, sanarwar ta baiwa jama'a tabbacin cewa, an dauki dukkan matakan da suka dace na kare rayukan fararen hula yayin wannan shiri.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China