in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalissar dattijan arewacin Najeriya ta yi barazanar gurfanar da gwamnati gaban kotun Hague
2013-05-15 09:52:58 cri

Majalissar dattijan arewacin Najeriya ko kuma NEF a takaice, ta yi barazanar gurfanar da gwamnatin kasar gaban babbar kotun hukunta laifukan yaki ta duniya dake Hague, bisa zargin kisan fararen fula, a cewar da majalissar rundunar sojin kasar ta yi a garin Baga, na jihar Borno dake arewa masu gabashin kasar.

Majalissar wadda ta gudanar da wani taro a birnin Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno, ranar Talata 14 ga watan nan ta ce, za ta gabatar da karar ne gaban kotun ta Hague, da zarar lauyoyinta sun kammala shirya takardun bincike da ake bukata.

Farfesa Ango Abdullahi, dake matsayin jagoran majalissar, ya ce, sun riga sun yanke shawarar daukar wannan mataki ne, duba da irin yadda sojojin kasar suka hallaka mutane da yawansu ya kai 200 a garin na Baga, ko da yake rundunar sojin ta ce, mutane 47 ne suka rasu, sakamakon arangamar da ta auku tsakaninsu da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram a 'yan kwanakin da suka gabata.

Har ila yau Ango ya ja hankalin jami'an tsaron kasar da su kaucewa amfani da karfi wajen yaki da kungiyar ta Boko Haram, yana mai cewa, daukar matakan shawarwari ne kadai hanya daya tilo da za a iya bi domin shawo kan matsalolin tsaro dake addabar wasu yankunan kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China