A ranar Laraba, kasar Najeriya ta yi alkawarin ba da karin taimakon kudi ga kasar Mali, wadda ta yi fama da yaki domin a samu sake gina kasar ta yammacin Afirka, bayan ta shafe watanni tana fama da rikici.
Mataimakin shugaban kasar Najeriya Namadi Sambo shi ne ya sanar da alkawarin yayin wani taron kasa da kasa dangane da bunkasa kasar Mali wanda kungiyar tarayyar Turai da gwamnatin rikon kwarya ta kasar Mali suka shirya a Brussels.
Mataimakin shugaban kasar Najeriyan ya ci gaba da cewa, Najeriya ta dage don ganin cewa, an maido da zaman lafiya da oda a kasar Mali kuma ta ci gaba da ba da tallafi na kudi da dai sauransu don tabbatar da cimma wannan buri.
Sambo ya yi amana da cewa, sake gina kasar Mali bayan yaki abu ne dake bukatar gagarumin goyon bayan kasa da kasa. Ya ce, wajibi a gano musabbabin rikicin da kuma fahimtar banbanci dake akwai tsakanin al'ummar kasar.
Ya kara da cewa, mun dage wajen tabbatar da hadin kai a arewacin kasar Mali ta hanyar shawarwari da tattaunawa, ta yadda za'a samar da damar bunkasar zamantakewa da tattalin arziki, don amfanin 'yan kasar Mali baki daya.
Ya zuwa yanzu dai, kasar Najeriya ta dage wajen samar da agajin bil adama da kuma na sake tsugunar da jama'a, gami da gudanarwa da kuma kula da ayyukan soji don a samu maido da zaman lafiya a kasar.(Lami)