A ranar Talata ne shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta baci a jihohi uku da ake fama da tashin hankali da ke arewa maso gabashin kasar.
A cewar shugaban na Najeriya, dokar ta bacin ta shafi jihar Yobe, jihar Adamawa, wato jihar tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, da kuma jihar Borno
Ko da ya ke shugabannin wadannan jihohin ne za su ci gaba da rike mukamansu, amma, jami'an tsaro ne za su tafiyar da harkokin tsaron jihohin, yayin da aka umarci babban hafsan tsaron kasar da ya hanzarta tura karin dakaru zuwa wadannan jihohi domin a kara inganta matakan tsaro.
An umarci dakarun da sauran jami'an tsaron da za a tura wadannan jihohi, da su dauki dukkan matakan da suka dace bisa ikon da aka ba su, don kawo karshe duk wasu hare-hare da ayyukan ta'addanci.
Shugaban na Najerriya ya ce, ya zama wajibi ga gwamnati ta dauki wannan mataki don dawo da zaman lafiya sakamakon irin abubuwan da suka faru na baya-bayan nan a wadannan jihohi.
Shugaba Jonathan dai ya yi wata ganawa da shugabannin tsaro game da karuwar tashin hankali a kasar, wanda ya yi sanadiyar rayukan sama da daruruwan mutane cikin kasa da wata guda.(Ibrahim)