Kafofin sufurin saman Najeriya sun bayyana cewa, wani jirgin saman soji ya fado a cibiyar sojin sama a jihar Rivers dake kudancin kasar ranar Alhamis da rana.
Kafofin da ba su so a bayyana sunayensu ba sun bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua cewa, jami'ai ba su tantance wadanda hatsarin ya ritsa da su ba, bayan da jirgin ya sauka a filin jiragen saman soji a garin Patakwal, ya kuma kama da wuta.
Zuwa yanzu dai mahukuntan sojin Najeriya sun ki cewa komai dangane da hatsarin ga 'yan jarida.
An samu aukuwar wannan hatsari ne a Najeriya ranar Alhamis, sa'o'i 72 bayan da wani jirgin sama shi ma mallakar sojin saman Najeriya, ya fado ranar Litinin a Niamey, babban birnin kasar Nijar, wanda ya yi sanadin rasuwar rayukan matuka jirgin guda biyu, ko da yake aikin da jirgin yake lokacin da ya fado bai shafi na yaki ba.(Lami)