Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu, ta yabawa ma'aikatan kasar yayin bikin ranar ma'aikata ta duniya da aka yi ranar Larabar 1 ga watan Mayun shekara ta 2013, saboda gudummawar da suka bayar wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
Ma'aikatan sun hallara a sassa daban-daban na kasar don bikin wannan rana da ake yi a ranar 1 ga watan Mayun ko wace shekara a kasar Afirka ta Kudu tun lokacin da kasar ta samu 'yancin kai a shekara ta 1994.
An kebe ranar ce a matsayin ranar hutu a kasar baki daya, inda ma'aikata ke hallara a wurare daban-daban domin su yi nazarin irin gwagwarmayar da suka yi game da neman yanayin aikin da ya dace da sauran hakkokinsu na aiki.
A cikin wata sanarwar da gwamnatin ta bayar a ranar Laraba, mai rikon mukamin kakakin gwamnatin kasar, Phumla Williams, ya yi kira ga ma'aikatan da su dauki matakan da suka dace wajen bunkasa tattalin arzikin kasar mai daurewa.
Sanarwar ta kuma bukaci ma'aikatu da su mutunta hakkokin ma'aikata, sannan kamata ya yi a yi bikin 'yancin ma'aikata da na 'yan kasa a kasar Afirka ta Kudu, ganin yadda tarihi a kasar ya nuna cewa, wadannan abubuwa ne da ba za a raba su ba.
Kakakin gwamnatin kasar ya ce, tattalin arzikin kasar ta Afirka ta Kudu ya karu da kashi 83 cikin 100 a cikin shekaru 19 da suka gabata, sannan gwamnati tana alfaharin fito da dokokin da ke kare ma'aikata daga hadarin aiki da kuma inganta yanayin aikinsu.
Don haka, sanarwar ta yi kira ga ma'aikatan, da su goyi bayan manufofi da shirye-shiryen gwamnati na rage talauci, samar da daidaito da kuma aikin yi.(Ibrahim)