Shugaban kwamitin Pinheiro ya yi nuni da cewa, kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa a rikicin kasar Siriya su fahimci cewa, a karkashin duk wani yanayi, ya zama dole a hana amfani da makamai masu guba. A ranar 5 ga wata, a birnin Geneva, mamban kwamitin bincike kan batun Siriya mai zaman kansa na M.D.D. Carrà Del Ponte ya ce, bisa kalamun shaidu da masu bincike na M.D.D. suka samu daga mutanen da rikicin Siriya ya rutsa da su da ma'aikata masu aikin jinya sun nuna cewa, an zargin bangaren adawa na Siriya da yin amfani da makamai masu guba a yayin wani dauki-ba-dadi da sojojin gwamnatin kasar.
Game da wannan, a ranar 6 ga wata, kakakin fadar White House Jay Carney ya bayyana cewa, Amurka ta nuna shakku game da zancen cewa bangaren adawa na Siriya yana da makamai masu guba ko kuma ya yi amfani da su, idan an yi amfani da makamai masu guba a Siriya, mai yiwuwa ne, mulkin Assad ya yi amfani da su, ya ci gaba da cewa, Amurka na da cikakkun shaidun cewa, ya kamata mulkin Assad ya dauki alhakin wannan lamari.(Bako)