in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira ga bangarorin da batun Siriya ya shafa da su kaucewa yin amfani da makamai wajen warware batun
2013-05-07 16:36:55 cri
Game da martanin da Siriya za ta aiwatar, sakamakon harin da Isra'ila ta kai mata, a ranar 7 ga wata, kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin na yin kira ga bangarorin da abin ya shafa, da su girmama cikakken yanki da mulkin kai na Siriya, su kuma zuciya nesa game da batun, kuma kada su yi amfani da makamai wajen warware batun, da magance daukar wasu matakan da za su tsananta halin da ake ciki, ta yadda za su dauki nauyi su kuma taka rawar gani wajen warware batun Siriya ta hanyar siyasa.

Kasar Sin ta bayyana cewa, hanyar siyasa ita ce daidaitaciyyar hanya daya tilo da za a bi don warware batun Siriya, sabo da haka, Sin ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa, da su girmama moriyar al'ummar Siriya, da gaggauta farfado da shawarwarin siyasa, a kokarin habaka harkokin siyasa a kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China