Kamfanin dillancin labaru na SANA na kasar ne ya bayyana shirin yin afuwa, kuma a cewarsa, dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki shi ne, don bikin tunawa da ranar samun 'yancin kan kasar, amma shirin bai ambaci yawan mutanen da za su amfana da afuwar ba.
Haka kuma, bangaren adawa ya nuna shakku game da shirin yin afuwar da gwamnatin Siriya ta bayyana.
Bugu da kari kuma, kamfanin dillancin labaru na Reuters, ya yi sharhin cewa, tun fara rikicin kasar ta Siriya, gwamnatin kasar ta bayyana shirin afuwa har sau da dama, amma bangaren adawa bai taba mayar da martani game da irin wadannan shirye-shirye ba.(Bako)