in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu ta yi kira da a kafa wani tsarin rigakafin yake-yake a Afrika
2013-04-27 12:13:06 cri

Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta yi kira a ranar Jumma'a ga kasashen Afrika da su kafa wani tsarin rigakafi domin yin rigakafin yake-yake a cikin nahiyar. Irin wannan tsari zai taimakawa kasashen Afrika gano matsalolin yake-yake da ka iyar faruwa, in ji ministar harkokin wajen Afrika ta Kudu madam Maite Nkoana-Mashabane.

Haka kuma ta bayyana cewa, abun farko ga kasashen Afrika shi ne na kafa da karfafa tsare-tsaren yin rigakafi.

'A matsayinmu na 'yan Afrika, mun san cewa, ya kamata mu kyautata hukumominmu domin fuskantar wadannan sauye-sauye dake adawa da tsarin mulki na gwamnati da lallashin salon dake tasowa na kungiyoyin tawaye da ba bisa doka ba, tare kuma da koma huldar abokantaka da gwamnatocin hadin kan 'yan kasa.' in ji ministar.

Madam Nkoana-Mashabana ta bayyana cewa, yake-yake sun rage sosai a tsawon karnin da ya gabata tun lokacin kafa tarayyar AU bisa tushenta na samar da zaman lafiya da tsaro. Don haka, ana iyar yin la'akari da raguwar yake-yake a kasashen Burundi, Sudan da Sudan ta Kudu, RDC-Congo da Somaliya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China