in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sanya batun kiyaye muhallin halittu cikin takardar bayani game da kare hakkin dan Adamu na kasar Sin
2013-05-14 17:57:37 cri



A ranar 14 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta fidda takardar bayani game da ci gaban da aka samu a sha'anin kare hakkin dan Adam a shekarar 2012 a kasar, inda ta bayyana kokarin da kasar Sin ta yi wajen kare hakkin dan Adam, gami da nasarorin da ta samu a wannan fanni. Wannan takardar bayani ta kasance ta 10 da kasar Sin ta fidda tun daga shekarar 1991, kuma a wannan shekara, an sanya batun kiyaye muhallin halittu a cikinta a karo na farko.


Wannan takardar bayani tana kunshe da kalmomi dubu 20 a ciki, inda aka yi amfani da alkaluma da hakikanin yanayi don bayyana sabon ci gaba da aka samu a batun kare hakkin dan Adam a kasar Sin daga fannoni guda 6, wato kare hakkin dan Adam ta fuskar siyasa, da tattalin arziki da al'adu, da raya zamantakewar al'umma, da kiyaye muhallin halittu, tare da yin mu'amala da hadin gwiwa da kasa da kasa wajen kare hakkin dan Adam.

Idan an kwatanta wannan takardar bayani da takardun da aka fidda a gabata, za a fahimci cewa, a wannan karo, an canja salon rubuta wannan takarda, mataimakin furfesa na cibiyar nazarin dokoki ta jami'ar Wuhan, Zhang Wanhong ya bayyana cewa, yadda a wannan karo, aka rubuta wannan takardar bayani ya nuna cewa, kasar Sin za ta dauki kwararan matakai don kare hakkin dan Adam daga dukkan fannoni, ya ce,"Takardar bayani ta farko kan kare hakkin dan Adam da kasar Sin ta fitar ta shafi hakkin rayuwa da hakkin samun bunkasuwa, amma yanzu, ana dora muhimmanci sosai game da kiyaye muhallin halittu, da raya al'adu, da zamantakewar al'umma, wannan ya nuna cewa, tunanin da kasar Sin ta yi wajen kare hakkin dan Adam yana kara dacewa da hakikanin yanayin da ake ciki."

Takardar ta bayyana cewa, bayan da aka sanya batun kare hakkin dan Adam cikin tsarin mulki na kasar Sin, da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar da kundin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, a watan Nuwamba na bara wato a yayin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis karo na 18, an mayar da batun girmama, da kare hakkin bin Adam, a matsayin wani muhimmin bangare na burin da ake kokarin neman cimmawa ta fuskar samun zaman wadata daga dukkan fannoni. Ban da wannan kuma, gwamnatin Sin ita ma, ta tsara shirin gudanar da ayyuka wajen kare hakkin dan Adam. Yanzu, an shiga wani sabon mataki wajen kare hakkin dan Adam a kasar Sin daga dukkan fannoni.

Abun da ya fi jawon hankalin jama'a shi ne, a cikin takardar bayani da aka fidda, an mayar da batun kiyaye muhallin halittu a matsayin wani muhimmin kashi. Furfesa Zhang Wei na jami'ar nazarin harkokin siyasa da dokoki ta kasar Sin ya bayyana cewa, wannan yana da ma'anar musamman, yana mai cewa,"Batun kiyaye muhalli ya shafi kowa da kowa, a lokacin da, kasar Sin ta lura cewa, yayin da ake raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma, kamata ya yi a mai da hankali wajen kiyaye muhallin halittu, sai dai da wuya a hada su tare. Amma, duk da haka, a wannan karo, an mayar da batun kiyaye muhallin halittu a matsayin wani babban burin da za a cimma game da kare hakkin dan Adam, a ganina, wannan yana da muhimmancin gaske ga kasar Sin da muke ciki a halin yanzu."

Ban da wannan kuma, a cikin takardar bayanin, an bayyana batun mu'amala da hadin gwiwa da kasar Sin take yi da kasashen duniya a harkar kare hakkin dan Adam a kasar. A cikin takardar, an ce, kasar Sin ta kara samun fahimtar juna, da koyon fasahohi daga juna, ta hanyar yin shawarwari da kasa da kasa wajen kare hakkin dan Adam.

Furfesa Zhang Wei ya bayyana cewa, game da batun kare hakkin dan Adam, kamata ya yi kasar Sin ta inganta yin shawarwari da ke tsakaninta da kasashen Turai da Amurka, wato kasashe masu wadata, don kara samun fahimtar juna da kawar da sabanin da ke tsakaninsu, a cewarsa, "Ya zama wajibi a kara yin mu'amala da shawarwari tsakaninsu, zargin juna da kushewa ba za su warware matsalolin da ake fuskanta ba, yanzu, kasar Sin na musayar fasahohi wajen kare hakkin dan Adam da kasashen yammacin duniya, kuma kasar Sin ita ma, ta yi fice wajen tsara wasu manufofi da daukar wasu matakai da suka dace, sabo da haka, yayin da suka yi mu'amala tsakaninsu, kasashen yammacin duniya su ma za su karu da wasu daga cikinsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China