Kamar sauran kudurorin da kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD ya zartas da su domin warware batun Syria, abu mafi muhimmanci cikin daftarin shi ne matsa lamba ga gwamnatin Syria, inda aka soki aikace-aikacen karya hakkin dan Adam da rundunar sojojin gwamnatin Syria da kungiyar Shabiha ta fararen hula masu makamai dake goyon bayan gwamnati suka aikata, amma, kusan ba a ambaci aikace-aikacen karya hakkin dan Adam da dakarun adawa da gwamnatin suka yi ba.
A yayin da aka tattauna kan kudurin, kasashen Rasha da Sin da dai sauran kasashe masu tasowa da yawa sun gabatar da cewa, kamata ya yi a sami daidaito tsakanin gwamnatin kasar Syria da kungiyar 'yan adawa, kuma a nuna ainihin halin da kasar Syria ke ciki tare da sasanta rikicin siyasar kasar yadda ya kamata.
Wakilin kasar Syria ya soki daftarin cewa, ana iya gano kiyayyar da wasu kasashen Larabawa ke nunawa kan Syria a cikin daftarin, hakan ya saba wa ka'idar shawarwari da hadin gwiwa na kwamitin kiyaye hakkin dan Adam na MDD, bugu da kari, ya kasa nuna wa jama'ar kasa da kasa hakikanin halin da kasar Syria ta ke ciki. (Maryam)