A yayin taron kwamiti na uku na MMD mai kula da harkokin zamantakewa, mutuntaka da al'adu, na babban taron MDD karo na 67 kan batun hakkin dan Adam, Mr. Wang Min ya nuna cewa, wasu kasashe na son sukar kasashe masu tasowa kan batun hakkin dan Adam, ta yadda suke kutsa kai cikin harkokin gida na wadannan kasashe, matakin da ke nuni ga karya ka'idojin MDD.
Wang Min ya jadadda cewa, kamata ya yi gamayyar kasa da kasa su mai da hankali kan kyawawan manufofin zaman rayuwa, da ikon samar da cigaba na kasashe masu tasowa, da kuma cika alkawarinsu na ba da taimako ga kasashen, bai kamata su yi ta suka kan batun hakkin dan Adam a kasashe masu tasowa ba.
Wang Min ya kuma yi kira ga gamayyar kasashen duniya, da su kau da ko wane irin rainin da suke nunawa. Ya ce, a kwanakin baya, zanga-zangar nuna rashin jin dadi daga bangarori daban daban ta rika tashi, sabo da wani fim da ya yi batanci ga addinin musulunci, kasar Sin ta mai da hankali sosai kan wannan batu, sabo da Sin na kin yarda da dukkanin manufofin da suka bata mutuncin addinin musulunci, bugu da kari, ya zama dole ga kasashen duniya, da su nuna kiyayya ga duk wani nau'in nuna wariyar kabila. (Maryam)