Hukumar kula da kare hakkin bil-adam ta MDD ta kara wa'adin aikin hukumar bincike game da Syria, wadda aka kafa a watan Satumban shekara 2011, yayin zaman ta na 21 a ranar 28 ga watan Satumba kana aka nada sabbin kwamishinoni guda 2.
Shugaban hukumar Paulo Pinheiro, ya ce ya yi farin ciki cewa, jami'in diflomasiyar nan dan kasar Swiss Carla del Ponte da kwararre kan gudanar da bincike dan kasar Thai Vitit Muntarbhorn sun shiga hukumar.
Ya ce yana fatan za su ci gaba da gudanar da binciken da suka saba tare da tattara shaidu da shari'a za ta yi amfani da su a nan gaba. (Ibrahim)