in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sha'anin aikin kare hakkin dan Adam na kasar Sin ya shiga wani sabon mataki
2013-05-14 12:50:23 cri

A ranar 14 ga wata, ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa na kasar Sin ya fidda takardar bayani game da aikin kare hakkin dan Adam na shekarar 2012, inda aka takaita nasarorin da kasar Sin ta samu wajen kare hakkin dan Adam. A cikin takardar bayanin, an ce, aikin kare hakkin dan Adam na kasar Sin ya shiga wani sabon mataki na samun bunkasuwa daga dukkan fannoni.

A cikin takardar, an yi amfani da alkaluma da abubuwa na zahiri don bayyana yanayin kare hakkin dan Adam a kasar Sin, inda aka bayyana cewa, girmama, da kare hakkin dan Adam buri ne na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da matakan da hukumomin kasar Sin suke dauka. Tun daga taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 da aka yi a watan Nuwamba na shekarar 2012, an mayar da girmama, da kare hakkin dan Adam wani babban jigo na samun zaman wadata daga dukkan fannoni a gida. Ban da haka, gwamnatin Sin ta zartas da shirin kare hakkin dan Adam, tare da yadda ake aiwatar da shirin.

A cikin takardar, an ce, babbar ka'idar da jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar ke bi wajen mulkin kasar ita ce, nacewa ga bin manufar raya kasa ta hanyar kimiyya da raya zamantakewar al'umma cikin jituwa, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da kawo alheri ga jama'a.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China