in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zabi mambobin kwamitin kare hakkokin dan Adam 18 a yayin babban taron MDD
2012-11-13 10:33:05 cri
A ran 12 ga wata, an zabi kasashe 18 a matsayin sabbin mambobin kwamitin kare hakkokin bil Adam na MDD ta hanyar kada kuri'un sirri, a yayin babban taron MDD karo na 67.

A yayin zaben, kasashe 15 daga yankuna 4 sun sami nasarar samun wakilci a wannan kwamiti, yawan kasashe dai mahalarta taron daga nahiyoyin Asiya, da Afirka, da Latin Amurka, da Turai ta gabas, da kuma yankin Caribbean, sun yi daidai da yawan kujerun da kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD ke da shi. Kasahen da suka samu wakilcin sun hada da kasashen Kwadivwa, Habasha, Gabon, Kenya da Saliyo daga nahiyar Afirka, sai kuma kasashen Japan, Kazakhstan, Pakistan, Koriya ta Kudu da kuma daular tarayyar Larabawa, daga nahiyar Asiya, da kuma kasashen Argentina, Brazil da Venezuela daga yankunan Latin Amurka da Caribbean, akwai kuma kasashen Estonia da jamhuriyar Montenegro daga Turai ta gabas.

Kasashe mahalarta guda biyar daga Turai ta yamma da sauran yankuna da suka hada da Amurka, Girka, Jamus, Ireland da Sweden, sun shiga takarar kujeru 3. inda kasashen Amurka, Jamus da Ireland suka sami nasarar samun wakilci a matsayin manbobin kwamitin na kare hakkin dan Adam na MDD bayan kada kuri'u.

Bisa doka dai, sabbin mambobin wannan kwamiti za su yi aiki ne na tsawon shekaru 3, tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2013 mai zuwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China