A ranar Talata, shuagaban Cote d'Ivoire, Alassane Ouattara zai halarci bikin bude taro da zai kwashe makonni biyu, da kuma zai karbi wakilan kungiyoyi masu zaman kansu 500 bisa taken "kwamitin Afrika kan kare hakkin dan adam da al'ummomi, shekaru 25 kan kokarin bunkasa da kiyaye hakkin dan adam a Afrika".
Ministan kare hakkin dan adam da 'yancin jama'a na kasar Cote d'Ivoire, ya bayyana cewa burin farko na wannan dandali shi ne na maido da martabar kasar Cote d'Ivoire game da batun kare hakkin dan adam, bayan tashe tashen hankalin siyasa da suka janyo babbar illa ga 'yancin dan adam a kasar.
Wannan haduwa ta Yamoussoukro za ta kasance tare da wasanni da za'a nunawa jama'a kan 'yancin dan adam da kuma mahawarori kan wannan batu, kuma shugabar wannan kwamiti, Catherine Dupe Atoki ta isa birnin Yamoussoukro tun ranar Jumm'a. (Maman Ada)