in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga Afirka ta Kudu da ta mai da batun farautar karkanda a matsayin wata annoba
2013-04-22 10:34:05 cri

A ranar Lahadi 21 ga watan nan ne jam'iyyar adawa ta "DA" a Afirka ta Kudu, ta yi kira ga mahukuntan kasar, da su dauki batun farautar dabbar karkanda da ake yi ba bisa ka'ida ba, a matsayin wani bala'i dake addabar kasar.

A cewar jigo a jam'iyyar ta "DA" Anthony Benadie, zartas da wannan kuduri zai taimaka matuka, wajen ba da damar amfani da kudaden da ake tanada, domin ba da tallafi yayin aukuwar annoba, wajen gudanar da ayyukun yaki da masu farautar namun daji ba bisa ka'ida ba.

Benadie wanda ya yi wannan tsokaci cikin wata sanarwa da aka rabawa 'yan jaridu, ya ce, ga dukkanin alamu, matakan da gwamnatin kasar ke dauka ba sa magance wannan matsala, don haka akwai bukatar daukar sabon mataki.

Daga nan sai Benadie ya yi kira da a janye dokar hana cinikin naman karkanda, yana mai ra'ayin dage dokar, zai ba da damar halastaccen cinikin wannan dabba, tare da bai wa al'umma, musamman ma manoma, damar shiga a dama da su, a kiwo da kuma tsaron wannan dabba.

Alkaluman lissafi da ma'aikatar lura da albarkatun ruwa da muhallin kasar ta fitar a wannan shekara da muke ciki, sun nuna cewa, a bana kadai, an hallaka karkanda kimanin 232, yayin da kuma kididdigar asusun kiyaye gandun daji na duniya ke nuna cewa, farautar wannan dabba ya karu da kaso 50 bisa dari tun daga shekarar 2011, yayin da mizanin awon karuwar wannan matsala ya yi tashin-gwauron-zabi da kashi 5,000 daga shekarar 2007 da ta gabata kawo wannan lokaci.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China