Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ba da umurni a ranar Alhamis ga samar da wani sabon taimako wato samar da dala miliyan 10 ga 'yan adawar kasar Syria. Ya sanya hannu kan wani kuduri da zai tamakawa sakataren kasa da kuma sakataren tsaro damar yin bincike da kiyasin duk wata ma'aikatar gwamnatin tarayya domin gaggauta samar da kayayyaki da ayyuka ga kawancen 'yan adawar Syria da kuma reshenta na soja.
Obama ya kare wannan mataki nasa bisa tsananin halin da ake ciki a kasar Syria da kuma kiyaye tsaron kasar Amurka.
Hukumomin Amurka sun ki su baiwa 'yan adawar kasar Syria makamai, bisa shakkun kada wadannan makamai su shiga hannu masu kaifin kishin Islama dake marawa gwamnatin Syria baya.
A birnin Landan, ministocin harkokin wajen kasashen G8 (Amurka, Birtaniya, Faransa, Jamus, Italiya, Japan, Canada da Rasha) sun kasa cimma matsaya daya wajen kawo karshen rikici a Syria da zai shiga cikin shekata ta uku. Amma duk da haka, sun dauki niyyar karfafa ba da taimakon jin kai ga wadanda suke bukata a kasar Syria. (Maman Ada)