in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da ayyukan samar da ruwan sha mai tsabta a jihar Zinder ta kasar Nijar
2013-04-01 10:51:41 cri

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou tare da jakadan kasar Sin dake Nijar mista Shi Hu sun kaddamar a ranar Lahadi a jihar Zinder dake gabashin, birni mafi girma na biyu na kasar da ayyukan karfafa samar da ruwan sha mai tsabta ga birnin da kewayensa. Birnin Zinder ya kasance tsofuwar hedkwatar kasar Nijar dake fama da matsalar ruwan sha mai tsabta tun fil azal, shi ma dalilin farko da ya sanya aka mai da birnin Niamey a matsayin hedkwatar kasar a shekarar 1922. Duk wani kokarin warware wannan babbar matsala ya sha kasa, amma a nan da 'yan shekaru fiye da biyu masu zuwa, za'a shawo kan wannan matsala da rancen kudi daga kasar Sin na kimanin Sefa biliyan 20.5 da aka samar a cikin watan Disamban da ya gabata, domin amfani da su wajen karfafa ayyukan samar da ruwan sha mai tsabta a birnin Zinder. Za'a gina wadannan rijiyoyi a tashar ruwa ta Gualaram dake karamar hukumar Oualelewa da Kassama a cikin jihar Damagaram Takaya masu nisan kilomita 61 da 80 daga birnin Zinder.

Baya ga birnin Zinder, an tsai da shirin samar da ruwan sha mai tsabta ga wasu kauyuka kimanin 40, kafa fanfunan jama'a 25 da hada gidaje dubu 200 ga wannan layi da kuma karfafa samar da ruwa ga birnin Mirriah. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China