Rahotanni da Al-Ahram, mallakar gwamnatin kasar Masar ta wallafa a shafinta na intanet na nuna cewa, aka sake komawa da tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak asibitin gidan yari na Tora a daren jiya Laraba.
A ranar Laraba da safe, babban mai gurfanar da masu laifi a kotu na kasar Talaat Ibrahim Abdullahi ya tsai da shawarar a sallami Mubarak daga asibitin soji na Maadi wanda ya fi inganci zuwa asibitin gidan yari.
Kotun daukaka kara ta kasar Masar ta sanya ranar 11 ga watan Mayu a matsayin rana da za ta sake shari'a kan tsohon shugaban kasa Hosni Mubarak da ministansa na harkokin cikin gida Habib Al-Adli, dangane da tuhuma da ake masu na kashe masu zanga-zanga, in ji rahotannin da Al-Ahram ta bayar.(Lami)