Babban alkalin kasar Amurka Eric Holder ya sanar a ranar Litinin din nan 22 ga wata cewa, an kai daya daga cikin wadanda ake zargi da kai harin Boston kotu kwanaki 7 da aukuwar wannan hari da ya hallaka mutane 3 ya kuma jikkata fiye da 200.
A cikin wata sanarwar da sashin shari'a na gwamnati ya fitar, an ce, Dzhokhar Tsarnaev, 'dan shekaru 19 da haihuwa ya yi bayyanar farko a kotu a ranar Litinin daga dakin asibitin Beth Israel, inda yake kwance kuma ana tuhumarsa da amfani da makaman kare dangi a kan mutane da kayayyaki.
Fadar gwamnatin Amurka tun da farko a ranar Litinin din ta sanar da cewa, ba za'a yi ma Tsarnaev hukunci a matsayin makiyi a shari'ar soji ba, sai dai a kotun gwamnatin tarayya.
Harin da ya auku har sau biyu a tsakar ranar Litinin din makon jiya dab da layin kammala tseren gudun yada kanin wani, kuma jami'an tsaro na FBI sun gano 'yan uwa biyu da hannu cikin wannan harin da shi Dzhokhar Tsarnaev, 'dan shekaru 19 da kuma yayansa Tamerlan Tsarnaev 'dan shekaru 26.(Fatimah)