A cikin sanarwarsa, Ban Ki-moon ya ce, ya ji farin ciki sosai da ganin Sudan da Sudan ta Kudu sun yi kyakkyawan shawarwari domin aiwatar da yarjejeniyoyin da suka daddale a birnin Addis Ababa a ran 27 ga watan Satumba a shekarar bara. Sa'an nan ya yaba wa shugabannin na kasashen 2 bisa aniyarsu ta ci gaba da himmantuwa wajen warware batun yankin Abyei, ya kuma kalubalance su kawar da sabani a tsakaninsu dangane da matsayin karshe na yankin na Abyei.
Har wa yau Ban Ki-moon ya yi maraba da maido da fitar da man fetur a tsakanin kasashen 2, a cewarsa kuma, lamarin ya kasance wata muhimmiyar alama ce ta daban a fannin kokarin maido da dangantakar da ke tsakaninsu yadda ya kamata, baya ga kafa yankin rashin daukar matakin soja a tsakaninsu da kuma gudanar da tsarin yin bincike da sa ido a kan bakin iyakarsu cikin hadin gwiwa. (Tasallah)