A yayin taron manema labarun da suka shirya cikin hadin gwiwa bayan shawarwari, shugabannin 2 sun jaddada cewa, tabbatar da samun tsaro, wani tushe ne wajen yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2, ta haka kasashen 2 za su himmantu wajen aiwatar da dukkan tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyar tsaron. Sa'an nan shugabannin 2 sun yaba wa juna kan matakan kokarin kafa yankin rashin daukar matakin soja a kan iyakarsu, sun kuma jaddada muhimmancin tawagar sa ido da kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU ta tura, wadda za ta sa ido kan aiwatar da yarjejeniyar tsaron.
Har ila yau shugabannin 2 sun nuna cewa, za su aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa da suka daddale a birnin Addis Ababa, a watan Satumba a bara, a kokarin inganta huldar da ke tsakanin kasashensu ta fuskar siyasa, tattalin arziki da cinikayya, za su kuma ci gaba da kokarinsu na warware dukkan batutuwan da ba su warware ba tukuna. (Tasallah)